ZIYARAR SHUGABAN KUNGIYA TA KASA ASH-SHEIKH IMAM ABDULLAHI BALA LAU A FADAR SARKIN HADEJIA DAKE GARIN HADEJIA.

A ranar lahadi 07 Muharram 1435/ 10/November/2013 bayan kammala Wa’azin kasa a garin Maigatari Shugaban Jibwis ya kawo ziyara ta musamman a fadar Mai Martaba Sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje.

Shugaban Yayi Wa’azi Mai Ratsa jiki akan tsoron Allah a cikin fadar, wanda sanda kowa yaji a jikin sa, yayi fatan alkhairi ga shi mai martaba, sannan yayi addu’a tare da ta’aziyya na rasuwar (Talban Hadejia) Marigayi Alhaji Abdulwahhab Tahir, yace wannan Duka Jarrabawa ce, da fatan Allah zai sa Muci Jarrabawar.

A nasa bayanan Mai Martaba Sarkin na Hadejia yai Godiya da wannan Ziyara, yace bazai manta da irinta ba, Yace Lalle Shugaba Bala Lau abokin aiki ne, yayi addu’an Allah ya maida su gidajen su lafiya.

Daga nan ya rako su suka shiga Motocin su suka hau
Hanya.

Sheikh Dr. Alhassan Sa’eed Adam Jos, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, Sheikh Dr. Abdullahi Saleh Pakistan da Eng. Mustapha Imam Sitti suna Daya Daga Cikin yan tawagar shugaban.

Allah ya tsare hanya ya kaimana Shugaban mu Gida Lafiya, tare da sauran jama’ar mu. Amin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *